explain-icon

Bayani

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna ganin yaƙi a tafarkin Allah da yakar maƙiya yana daga mafifitan ayyuka, sai Nana A'isah - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa zasu iya yin yaƙi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nuna musu mafificin yaƙi a cikin haƙƙinsu shi ne kubutaccen aikin Hajji wanda ya dace da AlKur'ani da Sunnah, wanda ya kubuta daga zunubi da kuma riya.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Yaƙi yana daga mafifitan ayyuka ga maza.
  • Hajji ga mata ya fi jihadi, kuma shi yana daga mafifitan ayyuka a gare su.
  • Ayyuka suna fifitar juna gwargwadan mai aikin.
  • An ambaci Hajji Jihadi; domin cewa shi jihadi ne na rai, kuma a cikinsa akwai bada dukiya, da ƙarfin jiki, shi ibada ce ta jiki da dukiya kamar yaƙi a tafarkin Allah.