Zainab 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta rasu, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga wurin matan da zasu yi mata wanka, sai ya ce da su: Ku wanketa da ruwa da magarya mara sau uku, ko sau biyar ko sama da haka, idan akwai buƙatuwar hakan, ku sanya wani abu daga kafur a na ƙarshen, idan kun gama to ku sanar da ni. Yayin da suka gama wanketa sai suka sanar masa, sai ya baiwa masu wankewar mayafinsa, kuma ya ce: Ku yi mata likkafani a cikinsa kuma ku sanya shi shi ne tufan da zai bi jikinta, sannan aka tufka gashin kanta tufka uku.