Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Lallai mu muna hawa jiragen ruwa a cikin kogi dan sū ko kasuwanci da abinda ya yi kama da hakan, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan wanda za'a iya sha, idan muka yi anfani da ruwan shan dan yin alwala da wanka zai ƙare, kuma ba zamu samu wanda zamu sha ba, shin ya halatta garemu mu yi alwala da ruwan kogi? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce game da ruwan kogi: Ruwansa mai tsarki ne kuma mai tsarkakewa; alwala tana halatta da shi da kuma wanka da shi, kuma halal ne cin abinda yake fita daga cikinsa na kifaye da wasunsu, koda an samu mushe ya fito a bayansa ba tare da an yi sū dinsa ba.