Xaya daga cikin Matan Manzon Allah SAW tayi Wankan Janaba, sai Manzon Allah SAW yazo zaiyi Al-wala ko wanka; sai yaso yayi amfani da ruwan da ya ragu na ruwan Wankan Matarsa -Allah ya yarda da ita- sai ta gaya masa cewa ita ta kasance tana da Janaba, sai ya nusar da ita cewa hakan ba zaiyi tasiri a ruwan ba, kasancewar sa mai tsarki kuma abun tsarkakewa