explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sallah ba ta inganta sai da karanta suratul Fatiha, ita rukuni ce daga rukunan sallah a kowace raka'a.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wanin karatun Fatiha ba ya isarwa daga gareta tare da iko a kanta.
  • Bacin raka'ar da ba'a karanta Fatiha a cikinta ba, daga mai ganganci da jahili da mai mantuwa; Domin cewa ita rukuni ce, rukunai ba sa saraya ta kowanne hali.
  • Karatun Fatiha yana saraya daga mamu idan ya riski liman yana ruku'u.