explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance lokuta da yawa yana yin asuwaki kuma yana umarni da a yi shi, hakan yana karfafuwa a wasu lokuta, daga cikinsu: Asuwaki lokacin tashi da daddare, lokacin da tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cuccuɗawa kuma yana wanke bakinsa da asuwaki.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Karfafuwar halaccin asuwaki bayan baccin dare, hakan domin barci yana hukunta canzawar bashin baki ne, shi kuma asuwaki shi ne kayan tsaftace shi.
  • Karfafuwar halaccin asuwaki a lokacin canjawar bashi a baki, dan yin riko da ma'anar data gabata.
  • Shar’antuwar tsafta ta fuskar gamewa, kuma ita tana daga sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma tana daga manyan ladubba.
  • Yin asuwaki a baki gabaɗayansa ya kunshi: Hakora, da dadashi, da harshe.
  • Asuwaki shi ne itacen da ake yanko shi daga bishiyar kirya ko waninta, ana anfani da shi a tsaftace baki da hakora, kuma yana daɗaɗa baki, yana gusar da warin da ba'a so.