Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga sharuddan ingancin sallah: Tsarki, to yana wajaba akan wanda ya yi nufin sallah ya yi alwala, in ya kasance wani abu mai warware alwala daga masu warware alwala ya faru agare shi; kamar bayan gida ko fitsari ko bacci ko wasunsu.