Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance tare da sahabbansa a wata liyafa ta abinci, sai aka kawo masa zira'in akuya kuma ya kasance shi ne mafi ƙayatarwar namanta gare shi , sai ya gutsiri wani gutsire da gefen haƙoransa sannan ya zantar da su, sai ya ce: Nine shugaban 'ya'yan Adam a ranar alƙiyama; hakan dan zantarwa da ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki -. Sannan ya ce: Shin kun san saboda me hakan? ya ce: Mutane za'a tarasu ranar alƙiyama a wata ƙasa mai faɗi madaidaiciya miƙaƙƙiya miƙewa ɗaya, waɗanda ke cikinta mai kira zai jiyar da su kuma mai kallo zai kewaye da su wani abu daga garesu ba zai ɓoyar masa ba; dan daidaituwar ƙasar a cikinta babu abinda wani zai ɓoyewa masu gani da shi, kuma gani zai zarce musu, yana nufin da ace mutum zai yi magana da mutum na ƙarshe zai ji su, ido kuma zai gansu, rana zata kusantowa halittu gwargwadan mil, kuma baƙin ciki da ɓacin rai zai riskesu abinda ba za su iya ɗauka ba kuma ba za su iya jurewa ba, sai su nemi tsira da ceto. Sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi wa masu imani ilhama cewa su zo wajen (annabi) Adam uban mutane, sai sū zo masa su ambaci falalarsa, wataƙila zai nema musu ceto a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, zasu ce masa: Kai ne Adam uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya sa mala'ikunSa sun yi maka sujjada, kuma Ya sanar da kai sunayen komai, kuma Ya yi busa a cikinka daga ranSa, sai ya yi hanzari sai ya ce: Lallai cewa Ubangijina Ya yi fushi a yau, fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, sannan ya ambaci kuskurensa, shi ne cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya hane shi cin bishiya sai ya ci, kuma zai ce: raina, shi ne wanda ya cancanci a nema masa ceto ku tafi zuwa wanina ku tafi zuwa Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu; sai su ce: Kai ne farkon Manzon da Allah Ya aiko shi zuwa mutanen ƙasa, kuma cewa Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, sai dai cewa shi zai yi hanzari: Cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, lallai cewa akwai wata mummunar addu'a da ya yi ta akan mutanensa, raina shi ne wanda ya cancaci a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Ibrahim. Sai su zowa (annabi) Ibarhim sai su ce: Kai ne badaɗayin Allah a cikin ƙasa, ka nema mana ceto zuwa Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai ya ce musu: Lallai cewa Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa yin irinsa ba kafinsa, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, kuma lallai haƙiƙa na kasance na yi ƙarya ƙarya uku; sune faɗinsa: Lallai ni mai rashin lafiya ne, da faɗinsa: Babbansu ne wannan ya aikata, da faɗinsa: Ga matarsa Saratu ki ba shi labarin cewa ni ɗan uwanki ne dan ya kuɓuta daga sharrinsa. Gaskiya cewa kalmomin uku kawai sun kasance ne a zunubin zance, sai dai yayin da surarsu suka kasance surar ƙarya sai ya ji tsoro daga garesu dan ƙanƙar da kai daga ceto; domin cewa wanda ya kasance mafi sanin Allah kuma mafi kusancin matsayi ya kasance mafi girman tsoro, sai ya ce: Raina shi ne wanda ya fi cancantar a nema masa haka, ku tafi zuwa wanina ku tafi zuwa Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda mu muke cikinsa?! sai ya ce: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushin da bai taɓa fushi irinsa ba kafinsa, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai cewa ni haƙiƙa na kashe wani mutum da ba'a umarce ni na kashe shi ba, raina shi ne wanda ya fi cancanta a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Isa ɗan Maryam. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: Kai (annabi) Isa kaine Manzon Allah, kuma kalmarSa da Ya jefata zuwa ga Nana Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfiɗar goyo alhali kana ƙarami, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai ya ce: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba ko sau ɗaya, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, bai ambaci wani zunubi ba, raina shi ne wanda ya fi cancantar a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Muhammad. Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce: Ya Muhammad Kai ne Manzon Allah kuma cikamakin Annabawa, haƙiƙa Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai in tafi sai in je ƙarƙashin al’Arshi, sai in faɗi ina mai sujjada ga Ubangijina - Mai girma da ɗaukaka -, sannan Ya yi mini buɗin wani abu na gode maSa da kyakkyawan yabonSa, bai yi taba buɗi ga wani a gabana ba kafin ni ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in ɗaga kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangijina, al'ummata ya Uabangijina, sai akarɓi cetansa. Sai ace masa: Ya Muhammad ka shigar da wanda babu hisabi a kansu daga al'ummarka ta ƙofar dama daga ƙofofin aljanna, kuma su abokanan tarayya ne a cikin koma bayan hakan na ƙofofi. Sannan ya ce: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai tsakanin sasanni biyu na ƙofa daga ƙofar aljanna, kamar tsakanin Makka da San'a'a ta Yamen ne, ko kamar tsakanin Makka da Busra ta Sham ne ita ce birnin Hauran.