Abu Burda - Allah Ya yarda da shi - ya hakaito cewa babansa Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya yi rashin lafiya, rashin lafiya mai tsanani har ya suma, kuma kansa ya zama a ɗakin wata mata daga cikin iyalansa, sai ta yi ihu ta yi masa kukan mutuwa, bai samu damar da zai mayar mata da komai ba saboda sumansa. Lokacin da ya farka ya ce: Lallai cewa shi ya kuɓuta (ya barranta) daga wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga gare shi, lallai cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - haƙiƙa ya kuɓuta daga: Al-Saliƙah: Ita ce mai ɗaga muryarta a lokacin musiba. AlHaliƙah: Ita ce wacce take aske gashin kanta a lokacin musiba. Asshaƙƙah: Ita ce wacce take tsaga tufafinta a lokacin musiba. Domin cewa su suna daga al'amuran Jahiliyya, kai an yi umarni da yin haƙuri a lokacin musiba, da neman ladanta ga Allah.