Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya kasance a zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wata ƙara daga sama kamar ƙarar ƙofar da aka buɗe, sai Mala’ika Jibril ya ɗaga kansa da idansa zuwa sama, sannan ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, kuma ba'a taɓa buɗeta ba sai yau ɗin nan, sai wani mala'ika daga cikin mala'iku ya sauko daga gareta zuwa ƙasa, bai taɓa sauka ba kafin nan sai yau, sai mala'ikan ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, kuma ya ce da shi: Ina maka bushara da haske biyu waɗanda aka baka ba'a taɓa bawa wani Annabi kafinka ba; sune: Suratul Fatiha, da kuma ƙarshen ayoyi biyu na Suratul Baƙara. Sannan mala'ikan ya ce: Wani ba zai karanta wani harafi daga garesu ba sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba shi abinda ke cikinsu na alheri da addu'a da kuma abin da yake nema.