explain-icon

Explanation

Annabi - - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana narko mai tsanani akan wanda ya dago kansa kafin limaminsa, Allah Ya maida kansa kan jaki, ko Ya maida surar halittarsa ta zama surar jaki.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Akwai halaye hudu ga mamu tare da liman: Uku an hana, su ne: Rigayarsa da daidai da shi da jinkirta masa. Abinda ya halatta ga mamu: Bin liman.
  • Wajabcin mamu ya bi liman a sallah.
  • Narko da canja surar wanda yake dago kansa kafin liman zuwa surar jaki abu ne mai yiwuwa, shi ne shafewa.