Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ruwa da abinda yake zuwa masa na dabbobi da zakokai, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa". Ingantacce ne - Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
explain-icon

شیکردنەوە

An tamnayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hukuncin tsarkin ruwa wanda dabbobi da zakokai suke zuwa domin su sha da makancinsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ruwa idan awonsa yakai manyan tulu biyu, su sun yi daidai da: Lita (210) cewa shi ruwa ne mai yawa ba ya najastuwa; sai dai idan ɗayan siffofinsa uku ya canja da najasa (su ne) launinsa ko ɗanɗanonsa ko warinsa.

explain-icon

لە سوودەکانی فەرموودەکە

  • Ruwa yana zama mai najasa idan ɗayan siffofinsa uku ya canza da najasa, launinsa, ko ɗanɗanonsa, ko warinsa, hadisin ya fita mafitar mafi rinjaye, ba wai akan iyakancewa ba.
  • Malamai sun yi ijma'ai akan cewa ruwa idan najasa ta canja shi to ya zama mai najasa kai tsaye, daidai ne ya kasance kaɗan ne ko mai yawa.