Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agate shi - ya bada labarin cewa kaɗai shi Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya aikoshi ne dan ya cika kyawawan ɗabi'u; inda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cika abinda ya gabace shi na manzanni, kuma mai cika kyawawan ɗabi'un larabawa, sun kasance suna son alheri kuma suna ƙin sharri, masu mutunci ne da karamci da gabata; sai aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cike abubuwan da suka gaza da ke cikin ɗabi'unsu, kamar alfaharinsu da nasabobi, da girman kai, da wulaƙanta talaka da wanin hakan.