Mummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.