Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa yaku musulmai duk wanda ya wayi gari a cikinku yana mai lafiyayye kuɓutacce a cikin jikinsa daga illoli da cututtuka, kuma yana amintacce a cikin ransa da iyalansa da hanyarsa ba ya tsoro, kuma yana da isasshen abin cin yininsa na halal; to kamar an tattara masa duniya ne gabaɗayanta.