explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin dokin da aka tanada dan tsere mai sauri a cikin gudunsa zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai tiƙe ga ƙarshen abinda ya karkace daga ressanta ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin yalwar aljanna, da girman bishiyoyinta.