Daga Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya ce Mun kasance a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: «Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?» Sai wani mai tambaya daga mazauna wajen ya tambaye shi: Ta yaya ɗayammu zai samu kyakykyawan aiki dubu? Ya ce: «Ya yi tasbihi sau ɗari, sai a rubuta masa kyakykyawa dubu, ko kuma a sarayar masa da kura-kurai dubu». Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin ɗayanku zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana? Sai ɗaya daga cikin mazauna a gurinsa ya ce: Ta yaya mutum zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana cikin sauƙi? Ya ce: To ya ce: "Subhanal Lahi". sau ɗari; sai a rubuta masa kaykkyawa dubu; domin cewa kyakkyawa ɗaya da kwatankwacinsa goma ne, ko kuma a kankare masa mummuna dubu daga cikin munanan ayyukansa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan falaloli; domin cewa su ne tsanin ayyukan biyayya.
  • Falalar tasbihi da zikiri, kuma cewa wannan aikin mai sauƙi ne wanda mutum ba zai ɗorawa kansa komai ba, da shi ne mutum zai samu wannan ladan mai girma.
  • Gaggawar sahabbai zuwa aikata aikin alheri ba tare da wani jinkiri ba.
  • Ninka kyawawan ayyuka zuwa kwatankwacinsu sau goma, hakan misalin faɗinSa ne - Allah Maɗaukakin sarki -: (Wanda ya zo da kyakkyawa to yana da kwatankwacinsa goma) [Al-An'am: 160], wannan shi ne mafi ƙarancin matakan ninkawa, inba haka ba ai tabbas haƙiƙa ya zo zuwa ninki ɗari bakwai.
  • Ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi canjin (Au (ko)) (Wa (da)) a cikin faɗinsa: Ko a sarayar masa... Al-Ƙari ya ce: Wau takan zo da ma'anar Au, dan haka babu saɓani tsakanin ruwayoyi biyun, kamar ma'ana: Cewa wanda ya faɗeta za'a rubuta masa kyakkyawa dubu, idan bai zamo a kansa ba sai a sarayar masa da wani abu a kuma ba shi wani abu, kuma zai iya yi wuwa Au ɗin ta kasance da ma'anar Wau, ko da ma'anar kai, to a wannan lokacin sai a haɗa tsakaninsu, kuma falalar Allah ta fi yalwa daga hakan ya ƙare, cewa shi za'a rubuta masa kyawawan lada dubu kuma a sarayar masa da munanan ayyuka dubu.