explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan yawaita ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, daga hakan (akwai): Tasbihi tare da Tahmidi.
  • Aljanna mai yalwa ce, kuma dashenta shi ne Tasbihi da Tahmidi, wannan falala ce daga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma ni'imominSa.
  • An keɓanci bishiyar dabino a cikin hadisin banda waninta cikin bishoyoyi; saboda yawan anfaninta da kuma daɗin 'ya'yanta; sbaoda haka ne Allah Ya buga misalin mumini da kuma imaninsa da ita a cikin Alƙur'ani.