explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya ci wani abinci da ya godewa Allah, babu wani iko gareni a samun abinci, ko a cinsa sai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma taimakonSa, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa wanda ya faɗi hakan bushara da cewa shi ya cancanci gafarar Allah gare shi a abinda ya shuɗe daga zunubansa ƙananu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • An so godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a ƙarshen cin abin ci.
  • Bayanin girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, inda Ya azirtasu kuma Ya sawwaƙa musu sabubban arziƙi , kuma Ya sanya kankare munanan ayyuka a cikin hakan.
  • Al'amuran bayi gabaɗayansu daga Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, ba da dabararsu ko ƙarfinsu ba, kuma bawa abin umarta ne da aikata sabubba.