explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya zagi ɗan uwansa musulmi, kuma hakan yana daga fasiƙanci shi ne fita daga yi wa Allah ɗa'a da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma yaƙar musulmi ga ɗan uwansa musulmi yana daga ayyukan kafirci, sai dai hakan kafirci ne ƙarami.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wajabcin girmama mutuncin musulmi da jininsa.
  • Girman lamarin zagin musulmi ba tare da wani haƙƙi ba; to mai zagin ba tare da wani haƙƙi ba fasiƙi ne.
  • Zagin musulmi da yaƙarsa yana raunana imani kuma yana tauye shi.
  • Sashin ayyuka ana ambatansu kafirci; koda basu kai ga kafirci babba mai fitarwa daga tafarkin Musulunci ba.
  • Abin nufi da kafirci a nan kafirci ƙarami wanda ba ya fitarwa daga Addini da haɗuwar Ahlus Sunnah; domin Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya tabbatar da 'yan uwantaka ta imani ga muminai a halin yaƙi tsakaninsu da kuma jayayyarsu, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce; {Idan ƙungiyoyi biyu ta muminai suka yi faɗa to ku yi sulhu a tsakaninsu} zuwa faɗinSa; {Kaɗai muminai 'yan uwa ne}.