Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.