Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta da wani wanda zai tsaya akan lamuran ta, da kuma miskini mabukaci, yana ciyar dasu yana mai neman lada a wurin Allah - Madaukakin sarki -, to shi a lada kamar mayakine a tafarkin Allah, ko kamar mai tsayuwa ne a sallar tahajjudin da baya gajiya, mai azimin da ba ya hutawa.