Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bayyana cewa ba masu shiga aljanna sai muminai, kuma imani ba ya cika, sannan halin jama'ar musulmai ba ya gyaruwa har sai sashinsu yaso sa shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya shiryar zuwa mafificin al'amuran da su ne soyayya take gamewa, ita ce yada sallama tsakanin musulmai, wacce Allah Ya sanyata gaisuwa ga bayinSa.