Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya ziyarci wani mara lafiya zai yi masa addu'a sai ya ce: Ya Allah (Ka tafiyar) Ka gusar da (tsanani) da tsananin rashin lafiya, (ya Ubangijin mutane) kuma Mahaliccinsu kuma Mai renansu, (Ka warkar da) wannan mara lafiyar (Kai ne) tsarki ya tabbatar maKa (Mai warkarwa) ina kamun ƙafa zuwa gareKa da sunanKa Mai warkarwa, (babu wata waraka) mai tabbata ga mara lafiya (sai warakarKa) da kuma lafiyarKa, (waraka) kai tsaye (wacce bata bari) ta wanzar ta kuma bar (wata masassara) da wani rashin lafiyar daban.