Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance idan ya yi nufin shiga aikin Hajji ko Umarah ita ce ya ce: (AmsawarKa ya Allah amsawarKa) amsawa ta lazimi gareKa bayan amsawa a cikin abinda Ka kiramu na ikhlasi da tauhidi da hajji da wasunsu, (AmsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa) Kaine Kai kaɗai wanda ka cancanci a bauta maka, baKa da abokin tarayya a rububiyyarKa da UluhiyyarKa da sunayenKa da siffofinKa, (lallai cewa godiya) da godiya da yabo (da ni'ima) daga gareKa Kaine Mai bada su (gareKa ne) ana juya su a kowane hali, (mulki ma) kamar haka naKa ne, (baKa da abokin tarayya) dukkansu naKa ne Kai kaɗai. Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: (AmsawarKa amsawarKa da taimakonKa) Ka taimakeni taimako bayan taimako, (alheri yana hannayenKa) dukkansa kuma daga falalarKa ne, (amsawarKa fata gareKa ne) da nema da tambaya zuwa wanda alheri yake a hannunSa, (aiki ma) gareKa ne Kaine wanda ya cancanci a bauta masa.