Idan musulmi ya yi nufin aikata wani al'amari daga abinda bai san ina ne daidai a cikinsa ba, to an shara'anta masa ya yi sallar Istikhara yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyawa sahabbansa - Allah Ya yarda da su - wannan sallar kamar yadda yake koya musu sura daga Alƙur'ani, sai ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya roƙi Allah yana mai cewa: «Ya Allah ni ina neman zaɓinKa» da neman dacewa da zaɓin al'amura biyu, kuma ina roƙonKa «da saninKa» mayalwaci wanda ya kewaye kowane abu, «ina neman ikonKa» Ka sanya ni mai iko inda babu wata dabara gareni kuma babu wani ƙarfi sai naKa «Da ikonKa» mai zarcewa Kai wani abu ba ya gajiyar da Kai, «Ina roƙonKa daga falalarKa» da kyautatawarKa «mai girma» mayalwaciya; yadda kyautarKa falala ce daga gareKa, kuma babu wani haƙƙi a cikin ni'ima ga wani a kanKa; «domin cewa Kai Kana da iko» akan dukkan komai, ni kuma mai rauni ne gajiyayye «bani da iko» akan wani abu sai da taimako daga gareKa, «Kai» "kana sani" da saninKa mai tattarowa mai kewayewa da zahiri da kuma badini, da alheri da kuma sharri, "ni" "bana sani" wani abu sai da dacewarKa da kuma shiryarwarKa, "Kai ne Masanin abinda ke boye" ilimi kai tsaye naKa ne, da iko mai zarcewa, babu haka ga waninKa sai dai abinda ka kaddara masa da kuma abinda Ka ba shi iko akansa. Sannan musulmi ya roƙi Ubangijinsa, ya ambaci buƙatarsa sai ya ce: «Ya Allah» ni na fawwala al'amarina gareKa «idan Kasan cewa» a cikin saninKa cewa wannan al'amarin «sai ya ambaci buƙatarsa» kamar siyan wannan gidan, ko a cikin siyan wannan motar, ko a cikin auren wannan matar mo wanin hakan... Idan wannan al'amarin ya kasance ya rigaya a cikin saninKa cewa a cikinsa «alheri ne a cikin Addini na» wanda shi ne igiyar al'amarina, «da rayuwata» a cikin duniyata «da ƙarshen al'amarina» da abinda al'amarina yake komawa zuwa gare shi, ko ca ya yi: «a cikin magaggaucin al'amarina da majinkircinsa» a duniya da lahira; «to Ka ƙaddara mini shi» Ka tanade shi Ka zartar da shi «gareni», kuma ka sawwaƙe shi «Ka sawwaƙe shi gareni», «sannan Ka yi albarka» kuma Ka yawaita alheri «gareni a cikinsa», «idan kuma Ka sani» ya Allah «cewa wannan al'amarin» wanda na baka zaɓi a kansa «sharri ne gareni a cikin Addini na da rayuwata da karshen al'amarina - ko cewa ya yi : A cikin magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - to Ka juyar da shi daga gareni nima ka juyar da ni daga gare shi , kuma Ka kaddara mini alheri a duk inda yake, sanann Ka yardar da ni da shi" da ma dukkan hukuncinKa daga abinda ka so da kabinda nake so da kuma abinda nake ki».