Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga riƙon karnuka, saidai dan buƙatar farauta, ko gadin dabbobi da shuka, wanda ya riƙe kare ga wanin haka kowace rana ƙiraɗi biyu zai ragu daga ladan aikinsa; kuma shi wani gwargwado ne sananne a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.