Adiyyu Dan Hatim ya tambayi Annabi dangane da farauta da karnukan farauta, kuma wanda mai shi ya koyar da shi, sai ya ce: kuma duk abinda suka kama maka idan dai ka ambai Allah akansa matukar dai baka samu wani karen tare da shi ba, idan ka sami wani karen tare da shi to kada ka ci domin kai ka yi bisimillah ne akan karenka kawai bakayi a daya karen ba, haka idan kai jifa da Mashi sai ya soki dabbar kuma jini ya futa duk wannan sabida yin Bisimillah, kuma idan gorar ce ta same shi ba tsini ba to kada ka ci, domin ya Mutu da bigewa ne sai ya zamo kamar wanda ya gangaro daga sama ko aka tunkuye shi, kuma idan ya cuna karensa kuma ya same shi da ransa to ya wajaba ya ranka shi a lokacin kuma ya zamanto halak ne kuma koda tare da wani karen suka kama, kuma ya tambaye shi game da farautar dabba da jifa da Mashi idan aka ambaci sunan Allah, sai ya Umarce shi daya ci kuma idan ya gudu ya kai kwana daya ko biyu kuma da yaganshi babu komai a jikinsa sa tabon Mashinka to ya halatta yaci kuma idan ya same shi ya nutse a ruwa to kada ya ci domin bai san mai ya kashe shi ba Mashinka ne ko kuma ruwan ne?