Jarir Ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi fitsari sannan ya yi alwala, kuma hakan ya wadatar da yin shafa akan huffinsa bai wanke ƙafafunsa ba, sai wanda ke gefensa Ya ce masa: Ya kake aikata haka?! sai ya ce: Eh, na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi fitsari, sannan ya yi alwala kuma ya yi shafa akan huffinsa. Jarir ya kasance ya musulunta daga baya-baya, bayan saukar Suratul Ma'idah wacce a cikinta ne ayar alwala take, yana mai nuni da hakan zuwa ga shafa akan huffi ba'a shafe hukuncin sa ba a wannan ayar.