Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tattaba agare shi - a lokacin yana huɗuba akan mimbari: Ya Manzon Allah ka sanar da ni yaya zan yi sallar dare? Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka yi sallah ka sallame daga kowadanne raka’oi biyu, idan ka ji tsoron ɓullowar asuba to ka sallaci raka'a ɗaya sai ta yi maka wutirin abin da ka sallata, kuma cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wasicci da a sanya ƙarshen sallar dare ta zama witiri.