Wannan Hadisin yana nuna cewa Manzon Allah SAW yayi Sallah a cikin Dare Sallar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani yana ta Maimaitata bai karanta komai ba sai ita, kuma a fili ita ce wannan Ayar da take cewa: "In kayi musu Azaba to su Bayinka ne kuma idan ka gafarta musu to kaine Mabuwayi kuma mai hikima" [Ma'ida: 118] kamar yadda yazo a wasu riwayoyin Hadisin