Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe wani tufafi na alhariri ko wani yanki daga gare shi, da hannunsa na hagu, kuma ya riƙe zinariya ta ado ko mai kama da ita, da hannunsa na dama, sannan ya ce: Lallai alhariri da zinariya, sanya su haramun ne akan maza, amma mata to su halal ne garesu.