Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar tsinuwa da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - akan nau’uka huɗu: Na farko: Mai yin ƙarin gashin kanta ko ga waninta da wani gashin daban. Na biyu: Mai neman a yi mata ƙarin gashi da buƙatar waninta cewa ya yi mata ƙarin gashi da wani gashin daban. Na uku: Al-Washimah ita ce wacce take aikin kafa allura a wani wuri na jiki, kamar fuska ko tafi ko ƙirji, sai ta sa kwalli ko makamancinsa a cikinsa, har sai gurbinsa ya yi shuɗi, ko ya yi kore; dan neman ado da kuma kyau. Na huɗu: Al-Mustaushimah ita ce wacce take son a yi mata zanen. Waɗannan ayyukan suna daga cikin manyan zunubai.