explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi maza daga sakin dukkan abinda yake suturce jikinsu tufa ne ko wanduna ko waninsu ƙasa da idan sawun diga-digai, kuma abinda ke ƙasan idan sawu na ƙafar mai mayafin da ya sake shi to shi yana cikin wuta dan yi masa uƙuba akan aikinsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hani daga tsawaita tufa zuwa abinda ke ƙasa da idan sawu ga maza, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  • Ibnu Hajar ya ce: An togance abinda ya sake shi ƙasa dan lalurara daga sakin mayafi; misali kamar wanda idan sawunsa akwai ciwon da yake cutar da shi idan bai rufe shi da mayafin ba inda bai samu waninsa ba.
  • Wannan hukuncin ya keɓanci maza ne; domin cewa mata an umarcesu da su saki mayafansu ƙasa da idan sawu har zuwa tsawon zira'i.