explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya, daga hakan: Na farko: Ciyar da dukiya a yaƙarsu; na siyan makamai da ciyarwa ga mayaƙa da makamancin hakan. Na biyu: Fita da rai da jiki dan haɗuwa da su da kuma tunkuɗesu. Na uku: Da kiransu ga wannan Addinin da harshe, da tsaida hujja akansu, da tsawatar da su da yi musu raddi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan yaƙar mushrikai da rai da dukiya da kuma harshe; kowa gwargwadan ikonsa, kuma yaƙi ba ya taƙaituwa akan yaki da rai kadai.
  • Umarni da yaƙi na wajabci ne, zai iya zama wajibi aini (akan kowa da kowa), kuma zai iya zama wajibi kifa'i (wasu sun ɗaukewa wasu).
  • Allah Ya shar’anta jihadi saboda wasu al'amura daga cikinsu: Na farko: Faɗa da shirka da mushrikai; domin cewa Allah ba Ya karɓar shirka har abada. Na biyu: Kawar da wahalhalun da suke bijirowa hanyar kira zuwa ga Allah. Na uku: Kiyaye aƙida daga dukkan abinda yake kishiyantarta. Na huɗu: Kariya ga musulmai da ƙasashensu da mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu.
explain-icon

Kari