Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwadaitarwa akan amsa wa ladani a lokacin jinsa, hakan da mu fadi irin abinda yake fada, jumla da jumla, A yayin da ya yi kabbara sai mu yi kabbara a bayansa, a yayin da ya zo da shaida biyu, sai mu zo da su a bayansa. An togance lafazin: (Ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa tsira) cewa za'a fada a bayansu: Babu dabara babu karfi sai ga Allah.