Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi aike zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Yaman da wani gutsire na zinari a cikin wata fata da aka jemeta da bagaruwa, gutsiren zinaren ba’a gama wanke shi daga ƙasarsa ba, ya ce: Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rarraba shi tsakanin mutum huɗu: Uyaina ɗan Badr al-Fuzari, da Aƙra'a ɗan Habis al-Hanzali, da Zaidul Khail al-Nabahani, da Alƙama ɗan Alasa al-Amiri, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mune mafi cancanta da wannan (kyautar) daga waɗannan, ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Shin ba za ku amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma". Sai ya ce: Sai wani mutum ya miƙe idanuwansa sun shige cikin raminsu, kuma kundukukinsa ya fito, mai babban goshi, kuma gemunsa mai kaurine ba mai tsawo ba ne, mai askakken kai, yana janye da zaninsa wanda yake rufe ƙasan jikinsa da shi, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Kaiconka, shin ba ni ne mafi cancantar mutanen dake doron ƙasa da jin tsoron Allah ba?!» Ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khali ɗan Walid ya ce: Ya Maonzon Allah, shin ba na daki wuyansa ba? Ya ce: A'a, wataƙila yana sallah, sai Khalid ya ce: Da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda babu shi a cikin zuciyarsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai cewa ni ba'a umarceni in bibiyi zukatan mutane ba ko in tsaga cikinsu ba; kaɗai an umarcenine in yi hukunci da zahirin al'amuransu, ya ce: Sannan ya kalle shi a lokacin ya juya baya, sai ya ce: Lallai wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan da sahabbansa ko ƙabilarsa masu yawan hazaƙa a karatun Littafin Allah da murya mai daɗi, harsunansu ɗanyu ne saboda yawan karanta shi, Alƙur'ani ba zai wuce maƙogwaransu ba, sai zukatansu su kiyaye shi sai su gyara shi, kuma Allah ba Zai ɗaga shi (gareShi) ba kuma ba zai karɓe shi ba, zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga baka da aka harba da sauri kuma a ɓoye. Kuma ina zatansa ya ce: Wallahi idan na riski tawayensu akan musulmai da takobi zan yaƙesu yaƙi mai tsanani kamar mutanen Samudawa.