Sarkin musulmai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa idan kuka ji ni ina zantar da wani hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lallai cewa ni banayin alkunya bana yin jirwaye mai kama da wanka kuma bana yin tauriyya, kawai ina magana ne ɓaro-ɓaro, kuma a ce in faɗo daga sama shi ya fi sauƙi a gurina daga in zantar da ku wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ina yi masa ƙarya, idan na yi magana a abinda ke tsakanina da mutane to lallai cewa yaƙi ɗan yaudara ne, saboda haka zan iyayin alkunya ko in yi jirwaye mai kama da wanka ko in yi tauriyya, haƙiƙa na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Wasu matasa zasu zo a ƙarshen zamani masu ƙananan shekaru, masu raunin hankula, suna faɗin (magana daga) Alƙur'ani kuma suna yawaita karanta shi, zasu fita daga Musulunci kuma su ƙetare iyakokinsa kamar yadda kibiya take fita daga abinda aka harba, imaninsu ba ya wuce maƙogwaransu, a duk inda kuka haɗu da su to ku kashesu, domin cewa kashesu lada ne ga wanda ya kashesu a ranar alƙiyama.