explain-icon

Explanação

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da sashin ni'imar aljanna, kuma lallai cewa mumini a cikin aljanna yana da wata shema mai girma mai yalwar ciki, ta gwal ɗaya wacce a cikinta akwai ƙofa, faɗinta da tsawonta a cikin sama mil sittin ne, a cikin kowane ɓangare da nahiya da kusurwarta daga cikin kusurwoyin ta huɗu akwai mata, sashinsu ba ya ganin sashi, mumini zai kewayesu.

explain-icon

Das notas do Hadith

  • Bayanin girman ni'imar 'yan aljanna.
  • Kwaɗaitarwa a kan aiki na gari ta hantar bayanin abinda Allah Ya tanadar musu na ni'ima.