Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya yi zatan cewa shi yana da wata falala akan wanda ke ƙasa da shi daga raunana saboda gwarzantakarsa da makamancin haka! Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin ana taimakonku ne kuma ana azirtaku ai sai saboda raunananku ta hanyar addu'o'insu da sallalolinsu da ikhlasinsu; domin su a galibi su ne mafi tsananin ikhlasi a cikin addu'a, kuma mafi yawan khushu'i a cikin ibada dan wofintar zuciyarsu daga rataya da ƙawace-ƙawacen duniya.