explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya sanya alhariri cikin maza a nan duniya ba zai sanya shi a lahira ba idan bai tubaba dan ukuba gare shi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Abin nufi da alhariri shi ne tataccen alhariri na dabi'a, amma alhariri na sana'antawa to Hadisin bai kunshe shi ba.
  • Haramcin sanya alhariri ga maza.
  • Hanin sanya alhariri ya game sanya shi da kuma shinfida shi.
  • An yi rangwame ga maza su sanya wani abu na alhariri a tufa da abinda bai ketare yatsu biyu zuwa yatsu hudu da za'a a yi alamomi ko ragowar tufa ba.