Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga sakin tufafi ko gwabso ƙasan idan sawu dan jiji da kai da kuma girman kai, kuma cewa wanda ya aikata hakan ya kasance ya cancanci narko mai tsanani cewa Allah ba Zai yi duba zuwa gareshi ba duba na rahama a ranar alƙiyama.