Annabi tshira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Umarni ai masa Zoben Dinare,ya kasance idan zai sashi yana sanya kansa cikin Tafinsa,sai Sahabbai suka bishi akan haka sukayi kamar yadda yayi,sannan bayan wani Lokaci Annabi tshira da Amincin Allah su tabbata agareshi ya zauna kan Minbari don Mutane su ganshi,sannan yace:Hakika na kasance ina sanya wannan Zoben,kuma ina sanya kansa acikin Tafina,sannan ya yarda shi yace:Na rantse da Allah bazan kara sashiba har abada,wannan ya faru ne bayan an haramtashi,sai Sahabbai suka jefar da Zobunansu saboda koyi da Manzan Allah tshira da amincin Allah su tabbata agareshi