Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi wa wani bulala sama da bulala goma sai dai a cikin saɓo, ba wai ana nufin cewa abinda ya zo a cikinsa na iyakance adadi daga mai shara'antawa na bulala ko duka ko uƙuba keɓantacciya ba, abin nufi ba'a yin ƙari a cikin bulalar ladabtarwa akan bulala goma, kamar yi wa mata bulala ko ɗa.