Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Nau'i uku na mutane zan yi rigima da su a ranar alƙiyama, duk wanda na zama abokin rigimarsa kuwa zan rinjaye shi: Na farko: Wanda ya rantse da Allah, ya yi alƙawari. sannan ya warware shi ya yi yaudara. Na biyu: Wanda ya saida ɗa akan cewa bawa ne, sai kuma ya ci kuɗinsa ya yi tasarrufi da ƙimarsa. Na uku: Wanda ya dauki ɗan ƙodago dan yin wani aiki, sai ya kammala masa aikin, amma bai biya shi kuɗin aikinsa ba.