Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku yi wa juna kyauta, za ku so juna».
Hasan ne - Buhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Abu Ya'la da Baihakisuka Rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan cewa Musulmi tare da ɗan'uwansa su dinga yawan kyaututtuka, kuma kyauta tana daga cikin sabubban soyayya da haɗuwar zuciya.
Daga Cikin Fa idodin Hadisin
An so yin kyauta; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ita.
Kyuata sababi ce ta (samun) soyayya.
Yana kamata ga mutum ya aikata dukkanin abin da zai jawo soyayya tsakakaninsa da mutane, daidai ne a kyauta ne ko a tausasa lamura ne, ko a magana mai kyau, ko a sakin fuska gwargwadan ikonsa.