Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya taimaki wani mutum akan jihadi a tafarkin Allah. sai ya bashi doki ya yi yaki a kansa, sai mutumin sai mutumin ya kasa ciyar da dokin, ba ya kula da shi, ya gajiyar da shu, har ya rame yayi rauni. Sai Umar yayi niyyar sayen dokin don ya san zai yi sauki sabo da ramewa da raunin da ya yi, sai dai bai yi cinikin dokin ba sai da ya shawarci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- game da haka,sai Annabi ya hana shi sayen dokin komai araharsa, saboda wannan abu ne da aka bayar don Allah, kar ka damu da shi,sai ya zama kamar ka dawo da wani bangare na abin da ka bayar ne, don ka riga ka bayar, kuma an kankare zunubanka, datti ya fita daga gare ka, bai kamata ya komo gareka ba, wannan shi yasa aka ambaci cinikin da suna kome duk da cewa saye zai yi.