Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani a yi sallar nafila a lokuta uku, ko a yi ƙabari a binne matattu a cikinsu: Lokaci na farko: Lokacin da rana zata fito a bayyane, hakan a yayin farkon ɓullowarta har sai ta ɗaga gwargwadan goron mashi, shi ana ƙaddara shi da kwatankwacin rubu'in sa'a (minti sha biyar). Na biyu: Lokacin da rana ta tsaya a tsakiyar sama, to babu inuwa gareta ta ɓangaren gabas ko yamma har sai ta karkace daga tsakiyar sama, inuwa ta bayyana daga ɓangaren gabas yayin da farkon lokacin sallar Azahar yake farawa, kuma taƙaitaccen lokaci ne; shi gwargwadan kwatankwacin minti biyar ne. Na uku: Loakcin da ta karkace rana ta fara faɗuwa har sai ta faɗi.