Annabi -tsira da amincin Allah- ya hana yin salla bayan Asuba har sai rana ta fito ta daga gwargwadon tsawon mashi yadda ido zai iya ganinta,gwargwadon minti biyar zuwa sha biyar,gwargwadon yadda malamai suka yi bayani.Haka nan yayi hani ga salla bayan La'asar har sai rana ta fadi,gabanin sallar Magariba da 'yan mintintina,,saboda yayi kamanceceniya da mushirikai wanda ke bautaw rana lokacin fitowar ta ko faduwarta,kuma an hana yin kamanceceniya dasu wajen ibada,har yace duk wanda yayi kama da wasu jama'a to yana cikinsu.