explain-icon

Bayani

Ya kasance daga shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yana farawa da asuwaki idan ya shiga gidansa a kowane lokaci da daddare ko da rana.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Halaccin yin asuwaki a game a dukkan lokuta, hakan yana ƙarfafa: A cikin lokutan da Shari’a ta so (a yi asuwaki) a cikinsu, daga garesu: A yayin shiga gida, da lokacin sallah, da lokacin alwala, da bayan farkawa daga bacci, da lokacin canjawar bashin baki.
  • Bayanin kwaɗayin tabi'ai akan tambaya game da halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sunnoninsa; dan su yi koyi da shi.
  • Ɗaukar ilimi daga ma'abotansa daga kuma wanda ya fi shi sani, inda aka tambayi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin shiga gida.
  • Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa, inda ya kasance yana tsarkake bakinsa a lokacin shiga gida.